1 Maris 2021 - 07:19
​Najeriya Za Ta Karbi Kashi Na Farko Na Allurar Rigakafin Corona A Ranar Biyu Ga Watan Maris

Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa, za ta karbi kashi na farko na allurar rigakafin cutar corona a ranar Talata mai zuwa.

ABNA24 : Sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya kuma shugaban kwamitin yaki da cutar corona da shugaba Buhari ya kafa, Boss Mustapha ne ya bayyana hakan a wata zantawa da wani gidan talabijin a daren jiya Asabar.

Boss Mustapha ya ce, an samu canji kan tsarin da aka yi na karbar rigakafin cutar corona, bayan wasu tsare-tsare na gaggawa da hukumar UNICEF ta yi, inda a halin yanzu Najeriya za ta karbi kashi na farko na wannan allura a ranar 2 ga watan Maris.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta gargadi mutanen kasar baki daya daga yin amfani da wani nau’in rigakafin cutar corona da ake rade-raden an shigo da shi kasar, wanda babu tabbaci a kansa.

Bayanin ya kara da cewa, hukumar NAFDAC ta amince da ingancin allurar rigakafin AstraZeneca, saboda haka Najeriya za ta fara da karbar kwalabe miliyan hudu na wannan allurar rigakafi, a kokarin da ake yi na ganin bayan wannan cuta baki daya a cikin Najeria.

342/